Translate to English

ZAYYANA (Preview)

Cover image


Honarabil Jatau ya yi turus sa'ar da ya ji ruwa yana zuba a cikin bandakin. Kirjinsa na dakan uku-uku ya shiga bandakin. A tsaye tana dubansa wata Mamarce.

"Ba ke na bari yanzu a daki ba?" Ya tambaya baki na rawa.

"Dani ka bari ka ganni anan?"

Jikin honarabil na rawa ya juya da baya zuwa cikin dakin.

"Wallahi har ka bani tsoro, ina ka tafi ka barni ni kadai a kwance?"

Wata Mamarce kwance akan gadonsa tana dubansa.

"Ba ke na gani yanzu a bandaki ba?"

"Da ni ka gani a bandaki za ka ganni a nan?"

Honarabil ya ji kamar an kwara masa ruwan sanyi.