Translate to English

Magajin Wilbafos Book 7: Chapter 755-659 (Kiru Sisiyu) (Preview)Bata karbi gorar ruwan ba har sai da ya gaji ya ajiye a gefe ya koma ya zauna.

"Ya... kike?"

Nostaljiya ta saki dariya mai ɗaci. Bayan kokarin kashe ta da sukai a lokuta sama da ɗaya, a yanzu kuma yana tambayar ta 'yaya take'.

"Bana..."

Ta daga masa hannu ya dakata. Ko kaɗan bata son jin labarin dazai faɗa.

"Mai ya kawo ka?"

Ya ɗan yi shiru yana kallon ta kafin ya gyada kai. Ya cancanci taji haushin sa saboda haka bai damu da duk wani furuci da zata yi masa ba. Bai san shirin mahaifin sa na kashe ta a lokacin yaƙin sarakunan jinzidal ba. To amma lokacin da abin ya faru yana kallo bai yi komai akai ba. Hasali ma ya goyi bayan mahaifin sa. Kuma har yanzu yana goyon bayan mahaifinsa, wanda hakan yasa yake ganin bai kamata ya nemi yafiya ba ko kaɗan.

"An saka ni na fitar dake daga wannan kurkuku na kai ki kwanar Jalsin dake kusa da garin Melmusa," inji Kiru.

Nostaljiya ta runtse ido cikin rashin fahimta. Bata san wani gari Melmusa ba, balle ta san kwanar Jalsin. Watakila ɗan-uwan nata ya fahimci haka saboda haka ya wuce gaba da bayani.