Translate to English

YANAYI NA YAU (Preview)

Ni maryam yar baba da mama.cike nake da nishadi a yau.Wannan rana na daya daga cikin ranakun da kowace mace ke ji dasu a rayuwar ta! Ranaku ne fararen tas! Da basa barin kwakwalwa.Yau na daya daga cikin ranakun Amarci na!Na dau wankana na Amarci na fito na zauna INA Tsara ado mai matukar burge ango na Salis tare da tafiya da hankalin sa.Na gama tsaf na Sanya kaya masu kyau da walkiya!

Dakina na kara feshe shi da turare mai dadin gaske! Zan fito kenan na hango wata takarda tana kokarin makale mun gefen gado ta zame mun datti! Ban yarda da kazanta ba a rayuwata! Don haka na tsugunna na dauko takarda! Wannan wace irin takarda CE da ban ganta ba a yayin da nayi sharar safe? Ina warware ta naga Ashe takardar banki CE wato

Sunan dake rubuce matsayin Wanda ya tura kudi har 50,000 sunan Ango na Salis.wadda aka tura ma kudin kuma Jamila Dahiru.Gaba na ya fadi ras! Na nemi gefen gado na zauna.Jamila Dahiru guda daya na sani.Itace babban kawata,itace Aminiya ta,itace yar uwata,itace uwata.karamar uwa abokiyar shan kanya.karamar uwata abar so na.Tare muka tashi tun muna yara.Kakata ce ta rasu,shine mama wacce take asalin bafulatanar chadi CE ta je ta taho da Momi Jamila gidan mu.Ni kuwa na sami abokiya da muka tare komai namu tare har girman mu. To meye Nasaban Angona Salis da momi na Jamila?Har da zai tura mata kudi har haka? Ko kuma ba ita bace? Don ban ga hadin biri da gada ba.Sannan for once momi Jamila bata boye mun komai.Babu Wanda yasan tsakanin mu.uwa UBA daga ni har ita bama kwance! Mum ishi juna rayuwa!

Shi kuma salis irin so da yake mun.Girman sa da Martaban sa.Bana tsammanin wai zai yi Wani ABU da momi Jamila bai sanar dani ba tukun.To wace alaka CE ma zasu yi ta kudi?

Abin dai ya daure mun kai.Na tashi na cigaba da shirin taryan Ango na.Auren mu sati biyu kacal muna ji da danyar love gara na tarairaye shi da kyau!

Amma duk da haka na kasa komai na dawo na dauko takardar INA kara dubawa cike da mamaki da al'ajabin Wannan al'amari!

Na zauna zaman jiran Momi na Jamila,shi kuma salis ya shiga dakin barcin mu wai zai canza kaya.A cikin shawarwarin da aka bani da zanyi aure,da yawa wadanda suka fini ilmi a cikin zamantakewar aure sunce kada na yarda ina duba wayar miji.Amma a yanzu ni banga mafita a gareni ba illa in duba wayar salis ko zan sami Karin haske!Don gaskiya ni ban San yadda zan sami amsoshin tambayoyi na ba kamar haka:

Wace Jamila CE wannan?Tawa CE dai Momi na ko wata Jamilar?

Idan wata CE,meye hadinta da Angina?Idan tawa CE,meye hadinta da salis?da zai bata kudi batare da sanina ba?sannan ita din me zatayi da kudi?A sanina tun tashin mu,mama bata barmu da rashi ba,balle kuma banana da ya dau momina Jamila Yar amana.

Gaskiya na shiga damuna,amma kuma da na tuna Allah, shi zan roka ya warware mun kon Allah zan roka ya warware mun komai.Nayi ajiyar zuciya,na Dan gincira zan dau remote in danna sai naji sallamar Momi na Jamila.Na tashi na taryo abata INA mai fàrinciki da ganinka.Ta kalle ni sama da kasa tace lallai kina Amarci! Kinga yadda kika kara kyau!Nace Momi nagode da tsokana.Muka bushe da dariya har da tafawa.muka zube kan kafet na cire dankwalina,Momi me zan kawo miki.Ba tare da bata lokaci ba tace ruwa mana,na kalleta muka kara tafawa.Naje kawo ma Momi ruwa INA kwankwanto a raina,anya Momi na CE kuwa salis ya turama kudi?