
RAYUWAR RAYHANAH 2
By SUMAYYAH ABDULKADIR 65 Downloads - No rating - 0 Sharhi Karanta a kan ₦ 300.00Game da Litaffin
J i ta yi kamar an dora mata dutsen Uhudu a kanta, sabida nauyin da kalamansa yayi mata, a gigice ta dago ta dubi Khalipha jikinta na bari na rudewa da gigicewa. Ta shiga waiwaye-waiwaye kada wai ko wani ya ji abinda Yaya Khalipha ya ce. Amma ga jin dadinta kowa harkar gabanshi yake yi da iyaye da ‘yan’uwansa nesa dasu sosai, don sai da ta ware kanta can nesa da jama’a kamin ta zauna. Shi kuwa Khalipha ko a kwalar rigarshi, bajewa ya kara yi a gabanta yana gaya mata duk kalaman soyayyar dake fitowa tun daga karkashin zuciyarsa ba daga fatar baki ba. Idanunshi a lumshe, ya yi kyan da bata taba lura ashe yana da shi haka ba.
Comments (0)
No comments