Game da Litaffin
Shin Matar Wane ne? Tsawon shekaru Almustapha da matarsa Lajja suna tare, suna matukar so da kaunar junansu, so irin na don Allah. Abubuwa biyu ne kadai ke damunsu a rayuwa; rashin haihuwa, da kuma wani lamari mai firgitarwa da ke tare da Lajja. Kwatsam wata rana tsaka a cikin ire-iren ranakun babi-babi na rayuwarsu, wani mutum mai suna Alhaji Hammad ya bayyana tare da shaidun cewar Lajja fa matarsa ce! Hujjojin da ya kawo sun tabbatar da abin da ya fada haka yake. Don haka alkali ta karbe Lajjar daga hannun Almustapha aka ba Alhaji Hammad. Shekara daya da faruwar wannan abu Allah ya yi wa Lajja haihuwa. To a wannan lokaci ne kuma wasu hujjojin suka kuma bayyana, kuma suka tabbatar wa duniya Lajja ba matar Alhaji Hammad ba ce! To matar wane ne?
Comments (0)
No comments